A cikin bayanin da rundunar ‘yan sandan kasar ta Ghana ta fitar, ta tabbatar da cewa an sace jakadan na Estonia a kasar Ghana Nabil Makram Basbous ne a cikin unguwar da yake zaune a lokacin da yake motsa jiki, kuma ana zatin cewa wasu ‘yan Najeriya ne su uku suka sace shi a safiyar Alhamis da ta gabata.
Sai dai rundunar ‘yan sadan ta kasar Ghana ba ta bayyana sunayen mutanen ba, amma ta ce tana da bayani a kansu, kuma tana ci gaba da bin diggin lamarinsu domin cafke su.
Wannan dai shi ne karon farko da aka sace jakadan wata kasa a kasar Ghana, wanda hukumomin kasar kuma suka zargi ‘yan Najeriya da aikatawa, duk kuwa da cewa mahukuntan Najeriya ba su ce uffan a kan batun ba.